Wata matar aure mai suna Hafsatu Yusuf wadda ta haifi ‘yan biyar a ranar Laraba a asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, ta rasu a safiyar ranar Alhamis sakamakon matsanancin zubar jini bayan haihuwa.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa wannan lamari mai tayar da hankali ya faru kasa da awanni 24 bayan da matar ta samu nasarar haihuwar jariran guda biyar, maza uku da mata biyu, lamarin da aka bayyana a matsayin abin mamaki kuma mai wuya a fannin kiwon lafiya.
Jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, Nabulisi Abubakar Kofar Naisa, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana cewa matar ta rasu ne sakamakon tsananin zubar jini bayan haihuwa.
Ya kara da cewa duk da kokarin da likitoci suka yi domin ceton rayuwarta, ba ta samu tsira daga wannan matsala ba.
Ya kuma bayyana cewa jariran guda biyar suna cikin koshin lafiya kuma suna samun kulawar likitoci yadda ya kamata a halin yanzu.
Gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyin kula da wadannan jarirai, inda ta tabbatar da cewa za ta samar musu da dukkanin kulawa da tallafin da suke bukata domin tabbatar da lafiyarsu da ci gabansu.
Kafin wannan haihuwa, Hafsatu Yusuf ta kasance tana da yara takwas, lamarin da ya kara nuna girman asarar da iyalanta suka yi sakamakon rasuwarta.












































