Wata babbar kotun tarayya a Abuja da ke ta bada umarnin kama tsohon ministan ayyuka na musamman Kabiru Tanimu Turaki (SAN).
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa kotun karkashin jagorancin mai shari’a Keke Meke ta kuma yi watsi da bukatar lauyoyin kare wanda ake tuhuma na soke tuhumar da ake masa.
Ana sa ran za a gurfanar da Turaki a gaban kotu ta hannun rundunar ‘yan sandan Nageriya karkashin jagorancin babban sufeton ‘yan sanda bisa zargin bayar da bayanan karya ga ‘yan sanda.
Tun da farko, an mika shari’ar zuwa wata kotu a Zuba, amma Turaki bai halarci zaman kotun domin amsa tuhumar da ake masa ba.
Daga bisani, tawagar lauyoyinsa ta shigar da korafi a kan alkalin tare da neman a sauya kotun da ke sauraron karar.
A hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis, mai shari’a Meke ya bayyana cewa babu wani uzuri da ya dace kan rashin halartar wanda ake tuhuma, yana mai cewa Turaki yana da cikakken sani kan shari’ar.
Saboda haka kotun ta bada umarnin a kamo shi domin ya gurfana a gaban kotu.
A yayin shari’ar, lauyan gwamnati Rabiu Umar ya yi adawa da bukatar lauyan kare wanda ake tuhuma Abdulaziz Ibrahim wanda ya bukaci kotun ta soke tuhumar.
An dage sauraron shari’ar zuwa ranar 22 ga Afrilu domin gurfanar da wanda ake tuhuma.













































