Shugaban Jami’ar Tarayya Kashere, Jihar Gombe, Farfesa Umaru Pate ya yi rashin mahaifiyarsa, Hajiya Zainab Pate.
Majiyar ‘yan uwa ta shaida wa ‘SolaceBase’ cewa Hajiya Zainab mai shekara 80, ta rasu ne a Yola, babban birnin jihar Adamawa ranar Laraba bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Ta rasu ta bar ‘ya’ya uku da suka hada da Farfesa Umar Pate da Amina da Hamza.