Kada ku yi harbi don raunata mutum, ku yi harbi don kisa ga duk wanda ya yi yunkurin kai hari gidan yari – Ministan ya umarci jami’ai

Aregbesola.fw
Aregbesola.fw

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya umarci jami’an gidan yari da su bindige duk wani da ya yi yunkurin kai hari a duk wani gidan gyaran hali a kasar nan daga yanzu.

Aregbesola ya ba da wannan umarnin ne a ranar Litinin yayin da ya ke duba wani gidan gyaran hali dake Agodi a Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Ministan ya ce dole ne jami’in su hana kowa kutsawa cikin ginin domin waje ne mai hatsari.

Ya ce duk wani harin da za a kai wa kowace cibiyar gyaran hali hari ne ga jihar don haka bai kamata a sake bari ba.

Ministan ya ce duk wani yunkuri na kai hari cibiyoyin gyara ya kamata ya zama na kunar bakin wake kuma ba za a bar masu aikata laifin su rayu su ba da labarin ba.

Ya ce, “Abu mafi mahimmanci shi ne rashin tsaro na wannan cibiyar. Sannan a tabbatar da cewa bata gari basu samu damar shiga cibiyar ba.

“Duk wanda yayi yunkurin karya tsaro a nan ya mutu. Kada ya rayu ya ba da labari. Wasu ne za su ba da labarinsa.

“Ba a yarda da duk wani ƙoƙari na keta kayan aikinmu ba. Kada ku yi harbi don raunata mutum, ku yi harbi don kisa.

“Wannan cikakken tsarin jihar ne don tabbatar da tsaron jama’a.

Idan dai za a iya tunawa, Aregbesola a wani taron manema labarai na kwanan nan da Ministan ya yi a fadar Aso Villa, ya bayyana cewa fursunoni 4,860 na gidajen gyaran hali na Najeriya ne suka tsere daga gidajen yari tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021 kadai, biyo bayan nasarar da aka samu ta kai hari a gidajen yari a Benin, Owerri, da Oyo, da dai sauransu.

Ya kuma bayyana cewa mutane 954 ne kawai aka sake kama su. Hakan ya faru ne gabanin harin da aka kai kwanan nan a gidan yari na Jos, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 9 tare da tserewa fursunoni 252.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here