Rundunar ‘Yan sanda ta jihar Kano ta gayyaci tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano Muaz Magaji wanda aka fi sani da Dansarauniya, wanda ya yi kaurin suna wajen Gwamna Ganduje da gwamnatinsa.
Muazu Magaji, ya tabbatar da gayyatar da aka yi masa cikin wasu bayanai da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Tsohon kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa, ya shahara a fadin kasar nan lokacin da Gwamna Ganduje ya kore shi daga mukaminsa bisa wasu kalamai da ya wallafa a shafukan sada zumunta kan rasuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari sakamakon kamuwa da cutar COVID-19.
Daga baya aka nada shi Shugaban Zartarwa, Aikin Bututun Gas na NNPC/AKK na Jihar Kano.
Sai dai an sake korar shi saboda abin da gwamnati ta kira rashin aikin yi da rashin biyayya.
Da yake tabbatar da gayyatar da aka yi masa, Muaz Magaji ya yi zargin cewa gwamnatin jihar Kano ce take masa bita da kulli, bayan ta yi yunkurin rufe shafinsa na Facebook amma hakan bai yiwu ba, shine suke kokarin razana shi ta hanyar amfani da ‘yan sanda.
Kakakin Rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatarwa da Solacebase cewa an gayyaci Muaz Magaji, inda ya bayyana cewa an gayyace shi ne domin amsa tambayoyi kan wata karar sa da aka shigar gaban kotu.
Kiyawa ya kara da cewa a gobe Talata ne ake sa ran Muaz Magaji zai bayyana a gaban rundunar domin amsa tambayoyi.












































