Majalisar kula da ‘yan sanda ta kasa ta tabbatar da Tunji Disu a matsayin IGP

Tunji Disu IGP (1)

Majalisar kula da ‘yan sanda ta kasa ta tabbatar da Olatunji Disu a matsayin babban sufeton ‘yan sanda na kasa (IGP), inda ta amince da nadin sa a matsayin shugaban ‘yan sanda na 23 a kasar.

Majalisar, karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da halartar gwamnonin jihohi, ta amince da nadin Disu a taron da aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Tun da farko a ranar 24 ga Fabrairu, Shugaba Tinubu ya nada Disu a matsayin mukaddashin IGP bayan murabus din Kayode Egbetokun.

Bisa tanadin kundin tsarin mulkin 1999 da dokar ‘yan sanda, nadin ya bukaci amincewar majalisar kafin ya zama cikakke.

Disu gogaggen jami’in dan sanda ne mai kwarewa na tsawon shekaru a bangaren aiki da gudanarwa.

Ya taba rike mukamin kwamishinan ‘yan sanda a jihar Rivers da Babban Birnin Tarayya, sannan ya rike mukamin mataimakin babban sufeto mai kula da sashen kare muhimman mutane da wurare na musamman.

Tabbatar da nadin nasa na nuna sauyin shugabanci a rundunar ‘yan sandan Najeriya a lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen tsaro a sassa daban-daban.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima; Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume; Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro Mallam Nuhu Ribadu; Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Ibrahim Geidam.

Sauran su ne, shugaban Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda Hashimu Argung; da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan jihar Kwara AbdulRazaq AbdulRahman, tare da wasu gwamnoni da mataimakan gwamnoni.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here