Hukumar Kula da Ayyukan Shari’a ta Jihar Jigawa (JSC) ta amince da tilasta wa alkalin kotun Shari’a, Sadisu Muhammad-Haruna, yin ritaya bisa laifin rashin da’a.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Hulda da Jama’a na JSC, Abba Wangara, ya fitar a Dutse ranar Talata, inda ya ce an yanke hukuncin ne bayan wani taro da aka gudanar a Dutse.
Ya ce bayan cikakken nazari kan korafi da hujjojin da aka tabbatar, hukumar ta yanke shawarar tilasta wa Muhammad-Haruna yin ritaya.
Ya kara da cewa bincike kan korafin da Abdullahi Hamza ya shigar ya nuna alkalin na da laifin cin hanci da tsare korafi ba bisa ka’ida ba.
Binciken ya kuma nuna cewa alkalin ya nemi kuma ya karbi wasu kudade daga mai korafi wadanda ba su cikin jadawalin kudaden kotu da dokokin Shari’a na Jigawa na shekarar 2012 suka tanada.
Hukumar ta ce wannan karbar kudade tare da tsare mai korafi ba bisa ka’ida ba babban saba wa ka’idojin aikin shari’a ne da kuma amfani da mukami ba daidai ba.
A cewar sa, hukumar ba za ta lamunci cin hanci ko amfani da iko ba, yayin da ta kuma amince da karin girma ga ma’aikata sama da 80 da nada wasu manyan ma’aikata a kotun daukaka kara ta Shari’a.













































