Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dawo Nijeriya a ranar Asabar shi da wasu daga cikin ministocinsa bayan sun halarci taron Makon Dorewar Cigaban tattalin arziki a Abu Dhabi na 2026.
Dawowar shugaban ƙasar ta biyo bayan halartar taron ne, inda aka gudanar da tattaunawa kan batutuwan tattalin arziki, makamashi da dorewar muhalli tsakanin ƙasashe.
A gefen taron, Nijeriya ta rattaba hannu kan Yarjejeniyar Haɗin Gwiwar Tattalin Arziki da Ƙasar ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, domin ƙarfafa alaƙar tattalin arziki tsakanin ɓangarorin biyu.
Yarjejeniyar ta ƙunshi zurfafa haɗin gwiwar tattalin arziki, bunƙasa cinikayya da zuba jari, ƙarfafa musayar fasaha, da faɗaɗa haɗin gwiwa a fannoni kamar makamashi, gine-gine, noma, hakar ma’adanai da makamashin sabuntawa.
A jawabin da ya gabatar a taron, Shugaba Tinubu ya sanar da shirya taron haɗin gwiwar zuba jari tsakanin Najeriya da Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa mai suna INVESTOPIA, wanda za a gudanar a birnin Legas a watan Fabrairu.
Shugaban ƙasar ya kuma bayyana burin Najeriya na tara Dala Biliyan 30 a duk shekara a fannin kuɗaɗen sauyin yanayi da masana’antar kore, yayin da ake hanzarta sauye-sauyen makamashi da faɗaɗa samar da lantarki a faɗin ƙasa.













































