Fiye da mabiya Ɗarikar Tijjaniyya miliyan 3 daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje sun hallara a jihar Katsina domin bikin Mauludin Sheikh Ibrahim Nyass a ranar Asabar.
Taron ya gudana ne a filin wasa na Muhammad Dikko da ke Katsina, inda ƙungiyar Majma’u Ahbab Sheikh Ibrahim Nyass ta shirya shi.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa shugabannin kwamitin shirya taron sun nuna hasashen zuwan baƙi kusan miliyan 4 daga jihohi 36 na ƙasar nan, har da Babban Birnin Tarayya Abuja, da kuma wasu ƙasashen Yammaci da Arewacin Afirka.
Wannan ya haifar da cunkoso mai yawa a cikin birnin Katsina tun kafin ranar taron.
Rahoton NAN ya nuna cewa kusan dukkan ɗakunan otal-otal da ke Katsina sun cika da baƙi da suka zo daga nesa, lamarin da ya sa wasu mazauna birnin suka buɗe gidajensu domin karɓar baƙi a matsayin nuna karamci.
Wasu daga cikin mahalarta da ba su samu masauki ba sun kwana a filin wasa duk da yanayin sanyi.
Kafin ƙarfe 9 na safe, filin wasan ya cika makil da jama’a, inda kujeru da fili gaba ɗaya suka cika, har ma da wuraren da ke kewaye da filin.
Haka kuma, babbar hanyar da ke haɗa wurin daga shatale-talen WTC zuwa a Barhin ta cika da jama’a.
Taron ya buɗe damar kasuwanci ga ’yan kasuwa, musamman masu sayar da abinci, ruwa, lemun kwalba, magungunan gargajiya, kayan sawa da littattafai, inda suka samu kasuwanci mai yawa a lokacin taron.
A jawabin da ya gabatar, Sheikh Ibrahim Dahiru-Bauchi ya gode wa gwamnatin jihar Katsina kan karɓar bakuncin taron tare da yin addu’o’i na zaman lafiya, kwanciyar hankali da wadata ga jihar, Arewa da Najeriya baki ɗaya.
Shi ma Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammad Sanusi II, ya ja hankalin Musulmi da su tsaya tsayin daka wajen bin umarnin Allah, neman ilimi da dogaro da kai ta hanyar sana’o’i.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya nuna godiya ga masu shirya taron bisa zaɓar jiharsa, tare da bayyana cewa irin waɗannan addu’o’i suna taimakawa wajen dawowar zaman lafiya a jihar.
Sheikh Muhammad Ibrahim-Nyass ya wakilci babban ɗan Sheikh Ibrahim Nyass wajen yin addu’a ga marigayi Sheikh Dahiru Usman-Bauchi, tare da kiran Musulmi a duniya da su zauna cikin haɗin kai da ƙauna, tare da riƙe Ɗarikar Tijjaniyya da ƙarfi.













































