Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da kafa kwamitin mutane 13 da zai gudanar da shirye-shiryen bikin cika shekara uku na gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan kuma Darakta Janar na Yada Labarai, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a, inda ya ce gwamnan ya amince da kwamitin don gudanar shirye-shiryen bikin murnar cimma wannan mataki na gwamnatin Gida Gida.
A cewar sanarwar, Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, zai zama shugaban kwamitin.
Sauran mambobin sun hada da Kwamishinan Ayyuka, Engr. Marwan Ahmad, Kwamishinan Lafiya, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr. Dahir Muhammad Hashim, Kwamishinan Ma’aikatar Noma da Albarkatun Kasa, Dr. Danjuma Mahmoud, da Kwamishinan Ilimi, Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda.
Haka kuma an nada Kwamishinan Kasa da Tsare-Tsare, Abduljabbar Umar Garko, Kwamishinan Raya Karkara da Ci gaban Al’umma, Abdulkadir Abdussalam; , Mai Baiwa Gwamna Shawara ta Musamman, Adda’u Lawan Kutama, Darakta Janar na Yada Labarai, Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa, Darakta Janar Protocol, Abdullahi Ibrahim Rogo, da Darakta Janar na Bincike da Adana Takardu, Hajiya Nana Asma’u Jibrin a cikin kwamitin.
Sanarwar ta kara bayyana cewa Alhaji Muhammad Jalo, Sakataren Bincike, Kimantawa da Harkokin Siyasa (REPA), zai zama sakataren kwamitin.
“Kwamitin an ba shi umarnin gudanar da shirin da ya dace domin murnar cika shekara uku na gwamnati da kuma nuna nasarorin da gwamnatin yanzu ta samu,” in ji sanarwar.
Ta kara da cewa ana sa ran Gwamna Yusuf zai kaddamar da kwamitin da misalin karfe 3:00 na yamma a ranar Juma’a a dakin taro na Ofishin Gwamnan.












































