Shugaban hukumar REMASAB Danzago ya rasu

IMG 20250213 WA0006 704x430

Allah ya yi wa manajan daraktan hukumar kwashe shara ta jihar Kano REMASAB Haruna Danzago rasuwa.

Majiya daga ‘yan uwansa tace ya rasu ne a safiyar ranar Alhamis a asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH) bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Danzago, ma’aikacin gwamnati ne, kuma dan siyasa mara tsoro, ya shahara da irin gudunmawar da yake bayarwa a harkokin siyasa a jihar Kano.

Gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya nada shi a matsayin Manajan Daraktan REMASAB a ranar 5 ga Yulin, 2023.

Majiyoyi sun ce za a yi jana’izar sa a kofar Kudu, fadar Sarkin Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here