Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
‘Yan Najeriya da dama sun nuna rashin jin dadinsu kan kudirin dokar da shugaban kasar Bola Tinubu ya sanya wa hannu a safiyar ranar Laraba.
‘Yan kasar a shafukan sada zumunta sun bayyana cewa ‘yan Najeriya na fuskantar wasu matsaloli da suka shafi hauhawar farashin kayayyaki da kalubalen tsaro.
Sun ce maido da tsohuwar wakar kasa ko taken kasa barbarewar abubuwan da suka sa a gaba ne.
Karin labari: Majalisar wakilan Najeriya za tayi taza da tsifa a CBN
Da yake yaba wa majalisar kasa a ranar Laraba, Tinubu ya ce “Don Allah, mu ci gaba da hada kai da gina kasarmu.
“Ba mu da wasu cibiyoyi ko hali da za su taimake mu sai dai mu yi da kanmu. Mu yi aiki tare don gina al’ummarmu ba don mu kaɗai ba” in ji shi.
Karin labari: Daraktoci 40 sun fadi jarrabawar cancantar zama sakatarori
Wakar wadda ‘yan Birtaniyya suka yi, ita ce taken Najeriya da aka yi amfani da ita tun daga samun ‘yancin kai a 1960 har zuwa 1978, inda aka maye gurbinta da wacce ‘yan kasa suka saba.
Ko da yake wasu mutane kalilan sun yaba wa shugaban da ya sanya hannu kan dokar, amma da yawa ba su ji dadin hakan ba.
A nasa bangaren, tsohon dan majalisar dattawa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya ce kamata ya yi majalisar ta fara tuntubar al’umma kafin ta sauya taken kasar.