YANZU-YANZU: Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim AbdulKadri ya rasu.

1c8e70c4 emir of gaya
1c8e70c4 emir of gaya

Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim AbdulKadri ya rasu.

Ajiyan Gaya, Malam Shamsu Kademi ya tabbatar wa Solacebase rasuwar marigayin.

Ya ce marigayi Sarkin, wanda aka haifa a shekarar 1930, ya rasu ne ranar Laraba sakamakon fama da rashin lafiya.

Sarkin ya rasu yana da shekara 91, kuma ya shafe shekara 30 yana kan karagar mulki.

Marigayi Sarkin ya hau gadon sarauta ne a shekarar 2019 bayan kirkiro masarautar Gaya, cikin masarautu hudu da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro

Za mu kawo muku karin bayani nan gaba kadan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here