Tinubu ya amince da karin mutane 50,000 domin tura su NYSC a 2026

nysc 1

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa NYSC, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da karin dalibai da suka kammala karatu 50,000 da za a tura yi wa kasa hidima a shekarar 2026.

Ya bayyana hakan a Abuja yayin kaddamar da asibitin da aka gyara a hedikwatar NYSC, a wani bangare na bikin cikar sa shekara guda a kan mukamin sa.

Ya ce amincewar wani bangare ne na kokarin magance jinkirin da ake samu wajen tura matasa yin hidimar kasa da kuma kara wa masu jiran shiga shirin damar samun gurbi.

Ya kara da cewa a cikin kasafin kudin shekarar 2026, an amince da karin mambobin masu yi wa kasa hidima 50,000 domin rage dogon lokacin jira da dalibai ke yi kafin a tura su.

Nafiu ya bayyana cewa tun bayan kafa shirin a shekarar 1973, NYSC ta samu gagarumin fadada, inda da karin da aka amince da shi ake sa ran za a tura mambobin masu yi wa kasa hidima 418,000 a shekarar 2026.

Ya ce karuwar cibiyoyin ilimi a fadin kasar nan ta taimaka wajen karuwar adadin daliban da ke kammala karatu, inda a shekarar 1972 cibiyoyin da ke samar da masu yi wa kasa hidima ba su wuce 10 zuwa 12 ba, kuma a wancan lokaci an tura mutane 2,364 kacal, amma yanzu akwai cibiyoyi sama da 400 da ke fitar da kusan dalibai 600,000 a kowace shekara.

Ya kuma bayyana cewa ba duk wadanda suka kammala karatu ne ke cancantar shiga shirin a kowace shekara ba, domin wasu na samun takardar kebewa, yayin da wasu kwararru kamar likitoci da lauyoyi ke kara yin wani horo kafin a tura su yin hidimar kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here