Rikicin Gabas ta Tsakiya na iya tilasta ‘yan Najeriya yin aiki daga gida — Dangote

Aliko Dangote new 750x430

Shugaban rukunin kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya yi gargadin cewa rikicin da ke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya na iya tilasta Najeriya da sauran ƙasashen Afirka su koma tsarin aiki daga gida irin na lokacin annobar COVID-19 idan rikicin bai lafa ba.

Dangote ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da shugaban ƙasa, Bola Tinubu, a gidansa da ke Ikoyi a Lagos, inda ya nuna damuwa kan yadda hauhawar farashin mai ke shafar tattalin arzikin nahiyar da tuni take fama da bashin da ya yi yawa.

Ya ce idan rikicin bai lafa ba, hakan zai yi tasiri sosai ga rayuwar al’umma a Afirka, inda mutane da dama ke dogaro da abin da za su samu a kullum domin rayuwa, kuma idan ba su yi aiki ba a rana guda, ba za su samu abin da za su ci ba.

Dangote ya kawo misalin yadda kasar Indonesia ta dauki matakai saboda matsin tattalin arzikin makamashi, inda aka bukaci ma’aikata su rika zuwa aiki kwana hudu kacal a mako, tare da la’akari da yiwuwar komawa tsarin aiki daga gida gaba ɗaya idan halin da ake ciki bai gyaru ba.

Ya kara da cewa idan wannan hali ya ci gaba, kasashe da dama za su iya daukar irin wannan mataki, kamar yadda aka yi a lokacin COVID-19, inda mutane suka koma yin aiki daga gida domin rage matsin tattalin arziki.

Dangote ya jaddada cewa Afirka za ta fi shan wahala a rikicin da ba ta da hannu a ciki, yana mai cewa hauhawar farashin makamashi da sauran kayayyaki zai kara jefa jama’a cikin wahala, musamman kananan ‘yan kasuwa da masu dogaro da janareto wajen gudanar da ayyukansu.

Ya yi kira ga daukar matakin gaggawa da kuma addu’o’i domin kawo karshen rikicin, yana mai cewa wajibi ne kasashen duniya su hada kai domin magance matsalar.

Dangote ya kuma yabawa ziyarar aiki da shugaban ƙasa ya kai ƙasar Birtaniya, yana mai cewa yarjejeniyar samar da ababen more rayuwa da aka kulla za ta bude sabbin damar kasuwanci da zuba jari ga Najeriya.

Ya kara da cewa wannan yarjejeniya za ta kara karfafa gwiwar sauran kasashe su zo su zuba jari a Najeriya, tare da bayyana cewa ‘yan kasuwar Najeriya yanzu za su iya samun damar tallafi daga hukumomin bada rance na kasar Birtaniya domin bunkasa ayyukansu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here