Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC a ranar Litinin sun mamaye wasu kadarori da ke da alaƙa da tsohon babban lauya na tarayya, Abubakar Malami, inda suka karɓe gidajensa da ofisoshinsa a wani mataki da bangarensa ya bayyana a matsayin ba bisa ka’ida ba kuma na siyasa.
Rahotanni sun ce wannan samame ya faru ne mintuna kaɗan bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya ziyarci gidan Malami.
A cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga Malami, Mohammed Bello Doka, ya fitar, ya zargi EFCC da yin aikin ba tare da sahalewar doka ba tare kuma da yin watsi da shari’ar da ke gudana a kotu.
Sanarwar ta bayyana cewa jami’an EFCC tare da jami’an tsaro dauke da makamai sun shiga wuraren da ƙarfi, suka yi musu alama tare da karɓe ikon wuraren ba tare da gabatar da wata takardar umarnin kotu da ta halatta hakan ba, inda kuma aka kama mutane biyu a yayin samamen.
Ofishin ya ce har yanzu shari’ar na gaban kotu a babban kotun tarayya da ke Abuja karkashin jagorancin Mai shari’a Joyce Abdulmalik, kuma babu wani hukunci na ƙarshe da kotun ta yanke kan lamarin.
Haka kuma ya jaddada cewa wani umarnin wucin gadi na kwace kadarori da kotu ta bayar a baya ya riga ya ƙare wa’adinsa, don haka ba zai iya zama hujjar wannan mataki da EFCC ta ɗauka ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa jami’an EFCC sun kasa gabatar da kowace takardar izini ta doka lokacin da aka nemi su yi hakan, tare da zargin cewa wannan mataki ya sabawa doka, cin zarafin iko ne, kuma wani yunƙuri ne na muzgunawa da bata sunan Malami saboda alaƙarsa da siyasa, duk da cewa yana goyon bayan yaƙi da cin hanci amma dole ne a yi hakan bisa tsarin doka.













































