‘Yan Sanda Sun Cafke Matar Da Ake Zargi Da Damfarar ‘Yan Kasuwa da Kudin Bogi a Kano

Fati Umar Dikko 1
Fati Umar Dikko 1

Yan sandan jihar Kano sun cafke wata mace mazauniyar unguwar Rijiyar Zaki mai suna Fati Umar Dikko, wadda ke amfani da shaidar biyan kudi na alert na bogi, bayan ta saye kayayyaki.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna-Kiyawa ya fitar.

A cewar Abdullahi Kiyawa, “ a ranar 12 ga watan Satumba, wasu ‘yan kasuwa 3, Jamilu Musa da Aliyu Inusa da Sadiya Muhammad, dake zaune a wurare daban-daban na jihar Kano, suka shigar da kara cewa, tsakanin ranekun 11 da 14 ga wata, wacce ake zargin ta sayi zannunwan da kudinsu ya kai N57,000 daga shagunansu”.

Ya ce bayan samun rahoton, Kwamishinan’yan sandan jihar Kano Sama’ila Shuaibu – Dikko, ya bada umarnin ga jami’an rundunar karkashin SP Daniel Amah da su binciko tare da cafke wacce ake zargin.

“Nan da nan suka shiga aiki, inda suka kai ga cafketa a yayin da take kokarin karbar wasu kayayyaki daga wasu shaguna ta hanyar da ta saba”

“Yayin binciken farko-farko, wadda ake zargin ta amsa aikata laifin, tana mai cewa, ta kware wajen kirkiro shaidar tura kudi na bogi domin damfarar mutane”

Solacebase ta ruwaito cewa, bayan cafketa da aka yi, an kara samun wasu korafe-korafe 4, daga Rita Rowland da Hauwa Sani da Ramatu Isa da Hadiza Abdullahi, dukkansu daga mabanbantan wurare, inda suk bayyana cewa, wadda ake zargin ta yi sayayya a shagunansu kamar haka

1. Kular zuba abinci da kudinsa ya kai Naira Dubu Tamanin N80,000.00
2. Yaduka da kudinsu ya kai Naira Dubu Dari Biyu da Talatin da Biyu N232,000.00
3. Zannuwa da kudinsu ya kai Naira Dubu Saba’in da Takwas N78,000.00
4. Leshi da kudinsa ya kai Naira Dubu Sittin da Biyar N65,000.00.

Abdullahi Kiyawa ya kara da cewa, za a gurfanar da matar a gaban kotu da zarar an kammala bincike. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here