An rantsar da Injiniya Abba kabir Yusuf a matsayin sabon gwamnan Jihar kano, a bikin da aka yi a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a birnin Kano.
An rantsar da shi tare da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.
Dubun dubatar magoya bayan jam’iyyar NNPP ne sanye da fararen kaya da jajayen huluna ga maza yayin da mata ke sanye da jajayen dan-kwali ko mayafi ko hijabi a wurin taron.
Sarakunan jihar ta Kano da jagoro kuma dan takarar jam’iyyar ta NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da sauran manyan baki ne suka halarci bikin.
Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya yi nasara ne a zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris inda ya kayar da dan takarar jam’iyya mai mulki, APC, Nasiru Yusuf Gawuna.













































