Zan Sake Nazari Kan Tsarin Sauya Fasalin Naira – Tinubu 

Bola Ahmed Tinubu sabo
Bola Ahmed Tinubu sabo

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin cewa gwamnatinsa zata sake nazari kan tsarin sauya fasalin naira wanda magabacinsa ya aiwatar. Tinubu ya yi wannan furucin ne a cikin jawabinsa na wurin bikin rantsarwa a filin Eagle Square da ke birnin tarayya Abuja ranar Litinin.

Sabon shugaban kasan ya ce tsoffi da sabbin takardun naira za su ci gaba da zama halastattun kuɗi a hannunn ‘yan Najeriya karkashin mulkinsa.

“Ya zama wajibi babban bankin Najeriya ya daidaita farashin musayar kuɗi. Wannan zai sauya akalae kuɗi daga hannun ‘yan canji zuwa zuba hannun jari mai amfani, kayayyaki da ayyukan da zasu bunƙasa tattalin arziki.”

“Muna buƙatar rage kuɗin ruwa domin ƙara yawan zuba hannun jari da sayen kayayyaki ta hanyar da tattalin aiziƙin mu zai habaka.” “CBN ya tsaurara wa mutane, koma wace irin manufa ce, tsarin sauya fasalin naira ya ƙara jefa talaka cikin ƙunci musamman idan aka yi la’akari da yawan waɗanda ba su da asusun banki a ƙasar nan.”

“Ya kamata mu sake nazari kan wannan tsari, amma a halin yanzu gwamnati na ta sahalewa ‘yan Najeriya su ci gaba da amfani da duka tsoho da sabo takardun naira,” inji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here