Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga wata ganawa da shugabannin tsaro da ministoci a fadar shugaban kasa da ke Abuja a safiyar ranar Juma’a, 8 ga watan Yuli. kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya rawatu cewa ganawar na da nasaba da farmakin da yan ta’adda suka kai gidan gyara hali na Kuje
An tattaro cewa akalla fursunoni 600 ciki harda mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram ne suka tsere a yayin harin.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor, shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Farouk Yahaya, shugaban sojin sama, Air Marshall Isiaka Amao, shugaban sojin ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo da Sufeto Janar na yan sanda, Usman Baba.
Yan majalisar shugaban kasa da suka halarci taron sun hada da ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, takwaransa na harkokin yan sanda, Mohammed Dingyadi
Sai ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi da ministan shari’a kuma Atoni Janar na tarayya, Abubakar Malami.













































