Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya sallami alkalin alkalan kasar Ghana sakamakon wani babban bincike da aka gudanar kan zargin karya bayanan shari’a da kuma karkatar da kudaden jama’a.
Kwamitin mutum biyar, karkashin jagorancin alkalin kotun kolin da Mahama ya kafa, ya kammala da cewa zarge-zargen da ake yi wa babbar jami’ar shari’ar kasar ya tabbata, tare da ba da shawarar a tsige ta.
“Bayan yin la’akari da koke-koke da shaidu, kwamitin ya gano cewa an kafa dalilan da suka nuna rashin da’a a karkashin doka ta 146 (1) kuma ta ba da shawarar tsige ta daga mukamin,” in ji mai magana da yawun shugaban kasar, Felix Ofosu, a wata sanarwa a ranar Litinin.
Birtaniya ta kori masu neman mafaka 44 daga Najeriya, Ghana
“Shugaba John Dramani Mahama ya tsige Alkalin Alkalan daga mukaminta ba tare da bata lokaci ba.”
Korar dai ita ce karon farko da aka binciki wani alkalin alkalai da ke ci gaba da zama a Ghana tare da korar daga mukamin.
Yayin da Mahama, wanda ya hau kan karagar mulki a watan Janairu, ya sha yin alkawarin karfafa yaki da cin hanci da rashawa, har yanzu babu tabbas ko babban mai shari’a, Gertrude Torkonoo, zai fuskanci shari’a.













































