Muna Binciken Gwamnan Zamfara Kan N70bn —EFCC

Matawalle sabo
Matawalle sabo

Hukumar Yaƙi da cin-hanci da Rashawa, EFCC, ta ce a halin yanzu tana tuhumar gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, bisa zargin almundahanar Naira biliyan 70bn.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, ta kuma tabbatar da cewa, har yanzu ana tsare da tsohon ministan wutar lantarki, Sale Mamman, wanda jami’an hukumar su ka kama a kwanakin baya bisa zargin almundahanar Naira biliyan 22.

Shugaban na EFCC, Abdulrasheed Bawa, ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a yau Alhamis, inda ya bukaci ƴan Nijeriya da su yi watsi da surutun da Matawalle ya yi na baya-bayan nan.

Gwamnan ya zargi Bawa kuma ya kalubalanci hukumar da ta bi ‘yan majalisar ministocin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Amma Bawa, wanda ya yi magana ta bakin Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar, Osita Nwajah, ya bayyana cewa bai kamata hukumar ta kula Matawalle ta hanyar mayar da martani ba amma ta yi hakan ne domin ta tauna tsakuwa.

“abin mamaki ne cewa Matawalle zai so ya dauki mukamin mai sa ido ta hanyar gaya wa EFCC wanda za ta bincika. Wannan yanayi ne na kamar a ce ”barawo” yana cewa kada a taba shi har sai an kama wasu ”barayi”?

“Abin takaici Matawalle ba shi da ikon ya bayyana wa EFCC wanda za ta kama, kuma a ina. Hukumar ta kama kowa da ga kowanne bangare na rayuwa ba wai zaɓe ta ke ba,” in ji shi

“A halin yanzu tsohon ministan wutar lantarki na hannun hukumar EFCC kan zargin almundahana da naira biliyan 22. Hakan bai ja hankalin Matawalle ba,” in ji Nwajah.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here