Na yi nadamar goyon bayan Tambuwal a majalisa ta bakwai – Gbajabiamila

347580310 1434615360632971 9222770796323441172 n
347580310 1434615360632971 9222770796323441172 n

Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya ce ya yi nadamar jagorancin tafiyar da ta bai wa Aminu Tambuwal nasarar zama kakakin majalisa ta bakwai a Najeriya.

Gbajabiamila ya bayyana nadamar tasa ne a lokacin da yake tsokaci kan ‘yan majalisar baya da ya taimaka mawa bayan adawa da zaɓin jam’iyya.

Shugaban majalisar ta wakilai, na yin waɗannan kalamai ne a wani zaman haɗin-gwiwa tsakanin sababbin ‘yan majalisa na APC da kuma sauran jam’iyyun adawa da ke shirin shiga majalisa ta 10 da zaran an ƙaddamar da ita.

Gamayyar ta amince da zaɓin da jam’iyyar APC ta yi na Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu a matsayin shugaba da mataimakinsa a majalisa ta 10.

Har yanzu ana ci gaba da gudanar da wannan zama a Transcorp Hilton, da ke Abuja.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here