Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya bada umarnin sake bude babban masallacin Ikare-Akoko wanda aka rufe tun ranar 18 ga Oktoba, 2022.
Aiyedatiwa ya bada wannan umarni ne a ranar Talata a Akure yayin wani taron buda baki na watan Ramadan da aka sanya wa suna Iftar tare da gwamna, wanda gwamnatin jihar ta shirya tare da hadin gwiwar hukumar kula da jin dadin Musulmi ta jihar.
Ya umarci Abubakar Muhammed Abbas, babban limamin garin kafin rufe masallacin, da ya ci gaba da jagorantar sallar Musulunci da sauran ayyukan addini a garin.
Gwamnan ya bayyana bude masallacin a gaban Sarkin gargajiya na Ikare, Oba Akadri Momoh, wanda shi ne Olukare na Ikare, da babban mufti da kuma babban limamin garin.
Ya kara da cewa babban limamin Ikare zai jagoranci sallar a masallacin cikin yanayi na soyayya da hadin kai.
An nada Abubakar a matsayin mataimakin shugaban kungiyar limamai da malamai ta jihar Ondo kwanan nan ta hannun wani kwamiti.
Kwamitin ya kasance karkashin jagorancin babban mufti na jihar Ondo, Sheikh Shehu Batuta.
An rufe masallacin ne a lokacin tsohon gwamnan marigayi Oluwarotimi Akeredolu domin dakile tashin hankali da ya samo asali daga rikicin shugabanci kan mukamin limanci.













































