Cikin Hotuna: Remi Tinubu ta ziyarci Babangida da Abdulsalami a Minna

Oluremi Tinubu and Babangida 750x430

Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, a ranar Talata ta kai wa tsohon shugaban kasar nan na mulkin soja Janar Ibrahim Badamosi Babangida ziyarar ban girma a gidansa da ke Minna, domin karfafa alaka da manyan kasa.

Ziyarar ta samu rakiyar Uwargidan mataimakin shugaban kasa Hajiya Nana Shettima don duba lafiyar sa tare da yi masa fatan alkhairi.

Bayan gajeruwar tattaunawa ne kuma suka shiga ganawar sirri, lamarin da ya haifar da sake tattaunawar da suka yi a bayan fage.

IBB 4 1 768x512

A ci gaba da ziyarar, Sanata Oluremi Tinubu ta kuma biyya gidan tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar, inda ya nuna jin dadinsa da ziyarar da ta yi.

“Abin farin ciki ne ganin uwargidan shugaban kasa ta zo duba lafiyata,” in ji Abdulsalami.

IBB 3 768x512

Haka kuma ta samu tarba daga uwargidan shugaban tsohon shugaban kasar.

Ziyarar ta nuna yadda Sanata Oluremi Tinubu ta jajirce wajen samar da kyakkyawar alaka mai karfi da shuwagabannin Najeriya da suka shude, tare da nuna muhimmancin hadin kan kasa da mutunta manyan kasa

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here