Fusatattun Mayakan Boko Haram Sun Yi Matan ‘Yan ISWAP 33 Kisan Gilla a Borno

e230a8d80e53796a
e230a8d80e53796a

Fusatattun mayakan Boko Haram sun halaka a kalla matan mayakan ISWAP 33 a dajin Sambisa domin daukar fansan kisan Malam Aboubakar (Munzir) da wasu mayaka 15 da aka halaka a wata muguwar artabu.

Tun ranar 3 ga watan Disamba, wani babban ‘dan Boko Haram dake kula da tsaunin Mandara, Ali Ngulde, ya jagoranci daruruwan mayaka dauke da makamai domin yakar ‘yan ta’addan ISWAP dake dajin Sambisa.

Farmakin ya fara ne bayan an yi kokarin yin sasanci tsakanin kungiyar Boko Haram da ta ISWAP kan cewa su shirya yin mubaya’a ga shugabannin IS/ISWAP.

 

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here