Hukumar Shirya Jarabawa Gama Sakandire Ta NECO Zata Fara Kai Jami’an Tsaro CIbiyoyin Jarabawa dake kasar nan

wassce 2
wassce 2

Hukumar shirya jarabawar ta kasa (NECO) ta ce za ta kawo karshen satar jarrabawarta ta hanyar tura jami’an hukumar tsaron farin kaya dake kare dukiyar al’umma (NSCDC) zuwa cibiyoyinta. Haka nan ma hukumar ta ce za ta hada da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) domin shiga cikin lamarin.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Ibrahim Wushishi wanda yake a matsayin babban shugaban hukumar NECO, ya bayyana irin ci gaban da aka samu a wajen wani taron karawa juna sani da aka gudanar a garin Uyo na jihar Akwa Ibom.

Shugaban hukumar ta NECO ya yi kira da a hada karfi da karfe domin magance matsalar tabarbarewar jarabawa. Wushishi ya ce akwai bukatar a gaggauta dakile matsalar domin tabbatar da ci gaban kasa baki daya.

“Saboda haka, wannan taron bitar ya yi la’akari da hanyoyi da za a iya amfani da su don dakile wannan barna da ta zama kamar cutar daji”

“Wannan halaryar na hana hazikan ɗalibai yin aiki tukuru, da ragewa takardar shaidar darajar ta, da kuma samar yan kasa nagari, kuma hakan na shafar bukatun al’umma”. “Don haka dole ne mu dauki shawarar hada kai da jami’an tsaro don kawar da wannan mummunar dabi’a.”

“Daga cikin jami’an tsaron Najeriya da muka amince muyi aiki da su sun hada da jami’an tsaro na Civil Defence wajen samar da tsaro a cibiyoyin jarabawa don hana miyagu/masu aikata munanan jarabawa,” in ji shugaban NECO”.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here