Harin gidan yari: Gwamnatin tarayya ta kara jaddada umarinin ta ga jami’an gidan yari da su kashe duk wanda ya kai hari

images 3 10
images 3 10

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, a ranar Litinin ya umarci hukumar kula da gidajen gyaran hali ta sauyawa Dakaru mata waɗanda ba zasu iya sheke mutum ba, wurin aiki. Ministan ya ba da wannan umarnin ne a wurin taron bayyana Sabon tambari da Kaki da kuma kaddamar da gidajen ma’aikata, ICT da Motocin Operation a Hedkwatar hukumar dake Abuja.

Da yake jinjina wa Jami’an, Aregbesola, ya nuna damuwarsa kan halayyar wasu jami’an gyaran hali, waɗanda ke cika wandonsu da iska idan ‘yan ta’adda sun kawo hari.

A cewarsa, Gidan yari ya zama wuri mai haɗari a yanzu kuma ya kamata Dakaru su yi harbe tare da sheƙe kowaye ya yi yunkurin kai hari wuraren.

“Bindigu ba kayan wasa bane, an tanade su ne don halaka ‘yan ta’adda, duk wani Jami’i da ba zai iya harbi da kisa ba, duk wani Jami’i da ba zai iya fasa kwanyar ɗan ta’adda ba, yana bukatar horo ko a sauya shi.”

“Bai kamata yan ta’adda su ji rauni kadai ba, duk wanda ba zai iya harbin da zai kisa ba, idan ba zaku iya korar su ba ku maida su Gidajen Yari na mata.”

“Duk wanda za’a aje a manya da matsakaitan Gidan Yari dole su zama masu tsauri. Mun sha fama da harin cikin mutunci ya zama wajibi mu dakatar da irin haka.”

Rauf Aregbesola yace mafi yawan ‘yan bindigan dake ta’addanci a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya fursunoni ne da suka tsero daga Gidajen Gyaran hali a jihar Imo. Ministan ya jaddada cewa duk wanda ya yi yunkurin kai farmaki gidan Yari a tura shi barzahu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here