Rikicin Sudan zai iya janyo yunwa mafi tsanani a duniya – WFP

Rikicin Sudan, WFP, yunwa, duniya
Hukumar abinci ta duniya WFP, ta yi gargaɗin cewa yaƙin da ake yi a Sudan zai iya janyo fitinar yunwa mafi tsanani a duniya, muddin ba'a kawo ƙarshensa ba...

Hukumar abinci ta duniya WFP, ta yi gargaɗin cewa yaƙin da ake yi a Sudan zai iya janyo fitinar yunwa mafi tsanani a duniya, muddin ba’a kawo ƙarshensa ba.

Fiye da wata 10 kenan ana gabza faɗa tsakanin ɓangarori biyu da basa ga maciji ga juna, lamarin da ya kai ga mutuwar kimanin mutane 14,000.

Karin labari: An shiga ruɗani bayan kisan limami a Zamfara

Haka kuma rikicin ya raba mutane miliyan takwas da muhallansu kuma mafiya yawan al’ummar ƙasar ba’a san me suke ciki ba, ga kuma ƙaruwar yunwa.

Yayin da ake ci gaba da faɗa, yawancin iyalai na ci gaba da tserewa zuwa ƙasashen da ke maƙwaftaka.

Inda su kan isa sansanoni ba tare da komai ba, cikin ja’ibar yunwa suna masu matuƙar buƙatar taimako.

Karin labari: Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano Ba Ta Da Ikon Binciken Bidiyon Dalar Ganduje – Kotu

Yayin wata ziyarar da ta kai wani sansani da ke Sudan ta Kudu, shugabar hukumar abinci ta duniya Cindy McCain, ta ce an manta da mutanen da yaƙin ya shafa.

Ta ce akwai buƙatar a baiwa hukumomin agaji damar kaiwa ga waɗanda rikicin ya keɓance don taimakawa waɗanda yunwa ta addaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here