Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan manufofin kasafin kuɗi da gyaran haraji, Taiwo Oyedele, ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa da fara aiwatar da sabon dokar haraji a watan Janairu na shekarar 2026, babu wata hukuma da ke da ikon cire kuɗi kai tsaye daga asusun bankin mutane, yana mai jaddada cewa tsoron cire kuɗi da ake yadawa ba tare da izini ba, ba shi da tushe marar inganci ne kuma barazana ne ga tsarin kuɗi.
Oyedele ya bayyana hakan ne a yayin wani taron tattaunawa da ’yan jarida a ranar Juma’a, inda ya nuna cewa duk da jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta, ba hukumar karɓar haraji ta cikin gida ta tarayya, ba babban bankin Najeriya, ba bankuna, kuma ba wata hukuma ta gwamnati da ke da ikon zare kuɗi kai tsaye daga asusun mutum ko na kasuwanci ba tare da bin doka ba.
Ya yi gargadin cewa yada bayanan ƙarya na iya haddasa firgici da janye kuɗaɗe daga bankuna, lamarin da ka iya girgiza tattalin arzikin ƙasa, yana mai tabbatar da cewa ko da mutum na da Biliyan ɗaya a asusunsa, babu wanda zai iya cire masa kuɗi kai tsaye.
Oyedele ya bayyana cewa a ƙarƙashin sabon dokar haraji, tsarin gudanar da haraji a Najeriya na buƙatar sanarwa, tantancewa, damar ƙalubalantar hukunci, da kuma duba shari’a a kotu kafin a ɗauki duk wani matakin tilastawa.
Karanta: Darajar naira ta yi faɗuwar da ba a taɓa gani ba
Ya ƙara da cewa doka na ba gwamnati damar neman Banki ya cire kuɗi ne kawai a cikin matsanancin yanayi, inda ake fuskantar manyan basussukan haraji da suka riga suka bi dukkan matakan doka, yana mai jaddada cewa wannan ba zai shafi yawancin ’yan Najeriya ba.
Oyedele ya kuma fayyace cewa buƙatar lambar tantance mai biyan haraji a asusun Banki ba sabuwar doka ba ce, domin tun dokar kuɗi ta shekarar 2020 aka samar da ita, sai dai sabon tsarin ya ɗaga iyakar rahoto daga Naira Miliyan 10 zuwa Naira Miliyan 25, wanda ya yi daidai da kusan Naira Miliyan 100 a matsayin kuɗin juyawar kasuwanci a shekara, lamarin da ke cire kashi 98 cikin 100 na masu asusun Banki daga wannan tanadi.
A cewarsa, an tsara gyaran harajin ne domin sauƙaƙa biyan haraji, ƙarfafa bin doka, faɗaɗa adadin masu biyan haraji, da kuma tallafa wa daidaiton tattalin arziki na dogon lokaci, yana mai nuna cewa Najeriya na da babbar damar sake farfaɗo da tattalin arzikinta daga shekara mai zuwa ta hanyar inganta ƙarfin sayayya da rage matsin hauhawar farashi.













































