Kotu ta dage karar da Marafa ya shigar yana kalubalantar zabukan da bangaren gwamna Matawalle suka gudanar a Zamfara

BD8B85CE E62A 4581 89F7 6D64B4940222
BD8B85CE E62A 4581 89F7 6D64B4940222

Mai shari’a Bello Kucheri na wata babbar kotun jihar Zamfara a ranar Alhamis ya dage ci gaba da sauraron karar da Sanata Kabiru Marafa  ya shigar kan jam’iyyar APC.

Marafa, jigo a jam’iyyar APC ya shigar da kara mai lamba ZM/GS/71/2022 inda ya nemi a soke zabukan APC da aka kammala a jihar.

Lauyan Marafa, John Shaka, ya roki kotun da ta bayyana cewa, zabukan mazabu dana kananan hukumomi da APC ta gudanar a Zamfara a matsayin haramtacce.

Ya bukaci kotun da ta soke zabukan kuma ta umurci jam’iyyar da ta gudanar da sabon zabe da zai ba da dama ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyar.

Ya zargi wadanda ake kara, APC da Gwamna Mai-Mala Buni Shugaban riko na APC na kasa da kwamitin babban taron jam’iyyar da yin watsi da dokokin jam’iyyar.

Marafa ya ce a matsayinsa na jigon jam’iyyar, yana da ‘yancin da tsarin mulki ya ba shi na kalubalantar zabukan da aka gudanar ba tare da bin tsarin mulkin jam’iyyar ba.

Ya ce, duk  da korafe-korafe da aka yi, jam’iyyar APC ta yi biris, inda ta shirya zabukan  ba tare da yin la’akari da matsalolin da jam’iyyar reshen jihar Zamfara ke fama da su ba.

Lauyan wadanda ake kara Ishiaka Dikko, ya nemi karin lokaci domin ba su damar shiryawa tare da gabatar da takardar shaidar bayyanar da sharudda.

Mai shari’a Kucheri  ya amince da bukatar da Ishiaka Dikko saboda babu wata takaddama daga kowane bangare.

Don haka ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 14 ga Maris don ci gaba da yin magana da kuma yiwuwar fara sauraron karar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here