Rahotanni na cewa an ga jinjirin watan azumin Ramadan a ƙasar Saudiyya a yau Juma’a, 28 da watan Fabrairu.
Shafin Inside the Haramain ne ya ruwaito hakan, inda ya ruwaito cewa, an ga jinjirin watan Ramadan na shekarar 1446 wato shekarar 2025 a Saudiyya.
Sanarwar ta ƙara da cewa gobe Asabar, 1 ga watan Maris ne za a fara azumin bana.
BBC