Tinubu ya maida martani game da sukar da sarki Sanusi yayi masa

Emir Sanusi Lamido and Bola Tinubu 750x430

 

Gwamnatin tarayya ta maida martani ga kalaman Sarkin Sanusi II, tana zarginsa da kokarin kawo cikas ga muhimman gyare-gyaren tattalin arziki saboda dalilan kashin kansa.

Gwamnatin ta jaddada cewa matsalolin da ake fuskanta yanzu sun samo asali ne daga shekaru masu yawa na lalacewar tsarin tattalin arziki.

Ta kuma bayyana cewa matakan da ake dauka kamar hada farashin canji da cire tallafin mai sun fara haifar da gagarumin ci gaba, ciki har da karuwar jari daga masu zuba hannun jari da karin kudi ga bangarorin ci gaba kamar ilimi da kiwon lafiya.

Gwamnatin ta bukaci Sarkin ya wuce matsalolin siyasa na kansa, tare da goyon bayan kokarin gyara tattalin arziki, tana mai kira ga hadin kai da tattaunawa don samun cigaban kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here