Za’a fara dawo da Alhazan Najeriya gida ranar juma’a, bayan kammala aikin Hajjin bana.
Shugaban hukumar alhazai ta kasa NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ne ya sanar da hakan yayin taron masu ruwa da tsaki na hukumar alhazan ta kasa da akayi shi a Saudi Arabiy ranar Laraba.
Hassan ya tabbatar da fara dawo da alhazai a kan lokaci duk dai matsalolin da aka fuskanata bana yayin jigilar alhazan.
Ya tabbatar da cewa NAHCON ta dau darasi akan matsalolin da suka faru, sanan zata dau matakan kare faruwar hakan a nan gaba.