‘yan bindiga sun kai hari kauyen Boto dake karamar hukumar Balewa a jihar Bauchi ranar Laraba, inda suka kashe mutum daya, sannan kuma sukai garkuwa da mutum uku.
Bayanin hakan na duake ciin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jiahr Bauchi, Ahmed Wakili, ya fitar yau Alhamis.
“jami’an mu sun bazama domin farautar masu garkuwa don tsairatar da wadanda akai garkuwar dasu.”
Ya kuma tabbatarwa da iyalan wadan da akai garkuwar dasu cewa zasu ceto su da yardar Allah.
Sanan kuma yayi kira ga mazauna kauyen dasu bawa jami’an tsaro hadin kai yayin gudanar da aikin su.