Jam’iyyar NNPP ta dakatar da shugabanta na jihar Bauchi

NNPP
NNPP

Uwar jam’iyyar NNPP ta kasa ta dakatar da shugabanta na jihar Bauchi, Alhaji Sani Shehu.

Skataran jam’iyyar mai wakilatar yankin Arewa masu gudu, Alhaji Babayo Liman, ne ya shaidawa manema labarai ranar Laraba a Bauchi.

Lima ya ce an dakatar da shugaban jam’iyyar na rukun kwaryan ne sakamakon girman kai, da rashin da’a da yake yiwa uwar jam’iyyyar ta kasa.

Ya kuma kara da cewa bayan uwar jam’iyyar ta kasa ta karbi korafin da aka shigar akansa, jam’iyyar ta tura masa da sammaci amma yaki karba.

ya kara da cewa Sakamakon haka jam’iyyar bata da wani zabi wanda ya wuci ta dakatar dashi, domin mu ciyar da jam’iyyar mu gaba.

Yayin da aka tuntubi shehu akan cire shin da uwar jam’iyyar tayi, ya ce bashi da masaniya akan cireshin.

“ Ni bani da wata masaniya akan dakatar dani, kuma har yanzu nine shugaban jam’iyyar a jihar Bauchi”

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here