Kotu ta rushe zaben fidda gwanin Jam’iyyar PDP a Jihar Ogun baki daya

PDP PDP 1
PDP PDP 1

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abeokuta, ta soke dukkan zabukan fitar da gwanin da jam’iyyar PDP ta gudanar a jihar Ogun domin zaben 2023.

Sai dai, ta ba da umarnin sake gudanar da sabon zaben fidda gwanin a cikin kwanaki 14 masu zuwa, kan cewa ba a bi dokar zabe ba a yayin zaben fidda gwanin.

Ta cikin wata takardar korafi da lauyan masu Kara Dr Kemi Pinherio SAN, ya shigar gaban Kotu, yace masu shigar da kara, Taiwo Olabode Idris da Kehinde Akala da Alhaji Ayinde Monsuru, sun garzaya kotu ne suna neman ta soke zaben fidda gwanin da jam’iyyar ta gudanar a ranar 25 ga watan Mayu, 2022 domin bai inganta ba.

Sun kuma roki kotu da ta umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) kan ta yi watsi da sakamakon zaben fidda gwanin da ake zargin babu sahihanci kuma babu adalci.

Masu shigar da karar, sun kuma bukaci kotun da ta bada umarnin a gudanar da wani sabon babban taro na musamman a jihar inda za a gudanar da zaben fidda gwanin jam’iyyar domin zabar dan takarar gwamna na jam’iyyar a zaben Shekarar 2023 dake tafe, ta hanyar amfani da jerin sunayen da hukumar zabe ta INEC ta tantance.

Alkalin kotun mai shari’a O.O Oguntoyinbo a hukuncin da ya yanke ya umarci jam’iyyar da ta sake gudanar da wani zaben fidda gwanin a cikin kwanaki 14 masu zuwa.

Lauyan masu kara, Pinherio, wanda Thaddeus Idenyi ya wakilta, ya ce Kotun ta soke zaben ne saboda an gudanar da shi ne da jerin sunayen wakilan wucin gadi.

Sakataren yada labaran jam’iyyar PDP a jihar, Akinloye Bankole ya ce jam’iyyar za ta yi nazari kan hukuncin kafin ta dauki mataki na gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here