Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya aike da sunayen mutum 19 gaban majalisar dattawa, domin tantance su a matsayin kwamishinonin zabe na jihohi.
Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan, shi ne karanta sunayen mutanen yayin zaman majalisar na ranar Talata, ta cikin takardar da Shugaban Kasar ya aike musu Mai kwanan wata 25 ga watan Yulin shekarar 2022.
A cikin wasikar, shugaba Buhari ya ce bukatar tabbatar da wadanda aka tura sunayen su ya kasance daidai da tanadin sashe na 154 (1) na kundin tsarin mulkin kasar nan.
Ya bayyana cewa biyar daga cikin kwamishinonin zaben sabunta tantance su za a yi, yayin da sauran 14 kuma sababbi ne.
Wadanda aka tura sunayen su don sabuntawa sun hada da Ibrahim Abdullahi (Adamawa) da Obo Effanga (Cross River) da Umar Ibrahim (Taraba) da Agboke Olaleke (Ogun) da Kuma Samuel Egwu, (Kogi).
Sauran mutum 14 su ne Onyeka Ugochi (Imo) da Muhammad Bashir ( Sokoto) da Ayobami Salami, (Oyo) da Zango Abdu (Katsina) sai Queen Agwu (Ebonyi) da Agundu Tersoo (Benue).
Haka kuma sauran wadanda za a tabbatar sun hada da: Yomere Oritsemlebi (Delta) da Yahaya Ibrahim (Kaduna) da Nura Ali (Kano) da Agu Uchenna (Enugu) sai Ahmed Garki (FCT) da Hudu Yunusa (Bauchi) da Uzochukwu Chijioke (Anambra) da Mohammed Nura (Yobe).













































