Hukumar Rarraba Wutar Lantarki ta Abuja (AEDC),ta sanar da nadin Mista Adeoye Fadeyibi a matsayin sabon Manajan Darakta/Babban Darakta.
Shugaban Hukumar AEDC, Mista Victor Osadolor ne ya sanar da nadin a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Talata.
Osadolor ya ce Fadeyibi, manaja mai gogewar gudanar da mulki sama na shekaru 20, ya gaji Mista Akinwumi Bada, wanda ya rike mukamin Manajan Daraktan riko na kamfanin.
Kafin ya koma AEDC, Fadeyibi ya kasance Manajan Daraktan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Eko (EKEDC).
Ya kasance babban Manajan Darakta a Transcorp Power Ltd, Ughelli, Delta inda ya inganta ayyukan kamfanin daga 164MW zuwa 634MW a cikin watanni 25.
AEDC ta kuma sanar da nadin Mista Kassim Burkullu a matsayin sabon babban jami’in fasaha (CTO), wanda ya maye gurbin Mista Oluwafemi Zacchaeus wanda ya yi aiki a matsayin babban jami’in fasaha na wucin gadi.
Burkullu, ƙwararren injiniya ne kuma masanin makamashi, yana gogewar aiki ta fiye da shekaru 25.
Ya koma AEDC ne daga Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Kano (KEDCO) inda ya zama Shugaban Sabis na Fasahar Fasahar Sadarwa.













































