An kwashe dukkan fasinjojin da harin jirgin kasa ya rutsa da su – Gwamnatin Kaduna

bomb train 1
bomb train 1

Gamnatin jihar Kaduna ta ce da safiyar yau ne jami’an tsaro suka kammala kwashe fasinjojin da suka makale a cikin jirgin kasa mai zuwa Kaduna daga Abuja.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Mista Samuel Aruwan ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Kaduna.

Ya ce jami’an Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA) da kuma kungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya na cikin aikin kwashe wadanda abin ya shafa.

Aruwan ya ce fasinjojin da suka samu raunuka da wadanda suka rasu an kai su asibiti.

Ya bayyana cewa an kwashe fasinjojin ne daga wurare daban-daban masu wuyar isarwa a cikin dazuzzuka da duwatsu a cikin Audujongom, daga hanyar Kaduna zuwa Abuja

“Kamar yadda aka bayyana a ranar Litinin, gwamnatin jihar Kaduna tana ci gaba da tuntubar Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) don tantance jerin fasinjojin da za a bi domin sa ido sosai,” in ji shi.

Kwamishinan ya ce Gwamna Nasir El-Rufai wanda ya yabawa duk wadanda suka halarci aikin kwashe mutanen ya kuma yi kira ga asibitocin da su rika kula da wadanda abin ya shafa da kyau.

Ya ce gwamnan ya kuma umurci ma’aikatar lafiya da ta tuntubi asibitocin domin gwamnati ce za ta dauki nauyin kula da lafiyarsu.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, wasu miyagu sun kai wa wani jirgin kasa fasinja da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja a daren ranar Litinin inda wasu fasinjoji suka jikkata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here