Harin Ta’addanci: Kamfanin AZMAN ya dakatar da zirga-zirga a filin jirgin sama na Kaduna 

Azman aircraft
Azman aircraft

 

Kamfanin jiragen sama na AZMAN ya dakatar da ayyukansa na zuwa filin jirgin Kaduna na wasu kwanaki bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai ranar Asabar a filin jirgin.

Solacebase ta bayar da rahoton harin da ‘yan ta’adda suka kai a filin jirgin a ranar Asabar din da ta gabata, wanda ya hana jirgin AZMAN da ke shirin zuwa Legas tashi.

Sanarwar ta dakatar da zirga-zirgar jiragen da ke zuwa filin jirgin ne a daren ranar Litinin da ta gabata ta hannun mahukuntan kamfanin.

Sanarwar ta kara da cewa, ”Mun fuskanci matsalar tsaro a kusa da filin jirgin, duk da cewa komai ya dawo dai-dai, amma ya zama wajibi mahukunta su sake tantance hanyoyin gudanar da ayyukansu a filin jirgin domin tabbatar da mafi girman tsaron kayan aiki, ma’aikata da fasinjoji.

A cewar sanarwar, ginshikin ayyukanmu aminci ne kuma za mu ci gaba da bincika kowane zaɓi don taimakawa isar da shi zuwa mafi girman matsayi.

Wannan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da ‘yan ta’adda suka kai hari kan titin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna a yankin Kateri-Rijana.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here