Majalisar Zartaswar Jihar Borno ta amince da sauya sunan Jami’ar Jihar Borno (BOSU) zuwa Jami’ar Kashim Ibrahim, domin girmama Sir Kashim Ibrahim, gwamnan farko na Arewa.
An yanke wannan shawarar ne a taron farko na 2025 da Gwamna Babagana Zulum ya jagoranta.
Kwamishinan Bayanan Al’umma, Farfesa Usman Tar, ya bayyana cewa za a fara amfani da sabon sunan bayan gyaran dokokin da suka kafa jami’ar da sanar da hukumomin da suka dace.
Haka kuma, majalisar ta amince da shirin ba wa tituna suna da lamba a Maiduguri da wasu birane, domin inganta tsare-tsaren birane.
A taron, Gwamna Zulum ya jaddada aniyar ci gaba da ayyukan farfado da jihar da inganta jin dadin al’umma a 2025.
An kuma yi wa shugaban ma’aikata mai ritaya, Barrister Malam Fannami, taron ban girma kan gudunmawarsa ga jihar.