Yanzu-yanzu: Kotu ta dakatar da babban taron jam’iyyar PDP saboda cire Lamido

Sule Lamido

Babbar Kotun tarayya da ke Abuja ta umurci jam’iyyar PDP da ta dakatar da babban taronta da aka shirya gudanarwa a birnin Ibadan na jihar Oyo a ranar Asabar da Lahadi mai zuwa.

A hukuncin da Mai shari’a Peter Lifu ya zartar, kotun ta kuma hana hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa gudanar da sa ido ko amincewa da sakamakon kowane taro da jam’iyyar za ta yi ba tare da haɗa tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido a matsayin ɗan takara ba.

Kotun ta bayyana cewa hujjojin da aka gabatar mata sun nuna an hana Lamido damar samun fom ɗin takarar shugabancin jam’iyya ta ƙasa ba bisa ka’ida ba, sabanin tsarin dokoki da ƙa’idojin jam’iyyar PDP.

Kotun ta kuma bayyana cewa jam’iyyar na da wajibcin samar wa mambobinta damar yin hidima ta hanyar tanadin hanyoyin da za su ba su damar cika burinsu a cikin tsarin shugabanci.

A matsayin umarni na dole, kotun ta bayyana cewa dole ne a dakatar da shirye-shiryen babban taron don bai wa Lamido damar karɓar fom ɗin takara, tarr da magoya bayansa da kuma gudanar da yaƙin neman zaɓe.

Wannan umarni ya tilasta dakatar da duk wani mataki da jam’iyyar PDP ke shirin ɗauka game da taron gangamin har sai an bai wa Sule Lamido cikakkiyar damar shiga jerin ’yan takarar shugabancin jam’iyyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here