Wike da jami’in Sojin Ruwa: tsoffin Sojoji sun buƙaci a sauke Ministan Abuja

WhatsApp Image 2025 11 11 at 2.25.36 PM 1 750x430

Tsoffin jami’an rundunar sojojin Najeriya da ke ƙarƙashin ƙungiyar haɗin gwiwar tsoffin jaruman soja a ranar Juma’a sun bukaci shugaban ƙasa Bola Tinubu ya kora ko ya sauke ministan Abuja, Nyesom Wike, saboda abin da ya faru tsakaninsa da wani jami’in rundunar sojin ruwa a birnin tarayya.

Ƙungiyar ta ƙunshi tsoffin manyan hafsoshi daga rundunar sojin ƙasa, na sama da ta ruwa, tare da bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga taƙaddama kan wani yanki na filin gwamnati da ake tsarewa bisa umarnin tsohon babban hafsan rundunar ruwa, vice admiral Zubairu Gambo mai ritaya.

Bidiyon da ya nuna Wike cikin fushi yana taƙaddama da jami’in wanda ya janyo ce-ce-ku-ce, kuma ƙungiyar ta gargadi cewa idan shugaban ƙasa ya kashe kunne, za su mamaye ma’aikatar birnin tarayya har sai an sauke Wike daga muƙaminsa.

A taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna, Kanal Yusuf Ibrahim mai ritaya ya ce kalaman da Wike ya yi wa jami’in rundunar ruwa sun ci mutuncin rundunar sojoji da kujerar da yake kai, sannan ya ce jami’in yana aiki ne bisa umarnin doka, don haka wulakanta shi tamkar wulakanta ikon gwamnati ne.

Ƙungiyar ta yaba wa ministan tsaro Badaru Abubakar, da karamin ministan tsaro Bello Matawalle, babban hafsan tsaro da sauran hafsoshin rundunar soja kan yadda suka tafiyar da lamarin cikin kwarewa.

Haka kuma wani memban ƙungiyar, Dakta Awwal Abdullahi, ya zargi Wike da yin ta’addanci da wulakanci ga jami’an soja a lokuta daban-daban, tare da barazanar cewa za su fito kan titi idan ba a dauki mataki ba.

Ƙungiyar ta ce aikinsa ya saɓawa mutuncin shugaban ƙasa, domin jami’in da ya wulakanta yana wakiltar ikon ƙasa.

Abdullahi ya ce Wike ya saɓa tsawatar da jami’an soja, ya kuma kwace kadarorin rundunar soji tare da rushe gine-ginen da suka shafi jami’an aiki da masu ritaya a runduna daban-daban.

Ƙungiyar ta bayyana cewa cire Wike daga muƙaminsa ba zai cutar da gwamnatin Tinubu ba, domin akwai mutanen da za su iya rike kujerar cikin mutunci, natsuwa da ƙwarewa.

Sun ce ma’aikatar birnin tarayya na wakiltar Najeriya gaba ɗaya, don haka wanda zai rike ta ya zama mai sanin ya kamata da kwarewar shugabanci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here