Majalisar dattawan Najeriya ta sake tabbatar da karin ministoci uku a kan guda 45 da ta amince da su a watan Agusta. Ministocin da majalisar ta tabbatar da su a ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba sun hada da Jamila Bio Ibrahim daga jihar Kwara; Balarabe Lawal daga jihar Kaduna; da Ayodele Olawande daga jihar Ondo.
Hakan na zuwa ne kwana daya bayan shugaban kasa Bola Tinubu ya aike wasika zuwa majalisar dattawan, inda ya nemi ta tabbatar da zababbun ministocin nasa.