Tsohon shugaban karamar hukumar Dala da ke jihar Kano da ya yi tsawon zango biyu Mahmoud Madakin Gini ya rasu.
SolaceBase ta ruwaito cewa, Madakin Gini, wanda ya jagoranci karamar hukumar zamanin mulkin Sanata Ibrahim Shekarau a tsakanin shekarun 2004 zuwa 2011, ya rasu ne sakamakon hatsarin mota a garin Kateri yau Litinin a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja kamar yadda wani daga cikin yan uwa da abokansa Umar Ladiyo, ya ce.
Wata saarwa da shugaban karamar hukumar Dala Surajo Ibrahim Imam, ya fitar ta ce za a gudanar da jana’izarsa da misalin karfe 5:00 na yamma a gidansu da ke unguwar Yelwa.













































