Shugaba Tinubu zai kai ziyara jihar Benue

Bola Tinubu scaled 1 750x430

Shugaban kasa Bola Tinubu, zai ziyarci jihar Benue a ranar Laraba domin lalubo hanyoyin da za a magance rikicin da ya addabi jihar.

Shugaba Tinubu, ya bayyana hakan ne a yau lokacin da ya ke kaddamar da sabon tsarin samar da ruwa a birnin tarayya Abuja watau Greater Abuja Water Supply Network wanda aka gudanar a birnin.

Mashawarci na musamman ga shugaban a fannin harkokin yada labarai Bayo Onanuga, shi ne ya bayyana hakan inda ya kara da cewa, shugaban ya maye gurbin ziyarar da zai kai Kaduna inda zai je jihar ta Benue a kokarinsa na ziyartar yankunan da ke fuskantar matsalolin rikice-rikice don shawo kan matsalar.

Onanuga yaq kara da cewa, manufar ziyarar shi ne don magance rikicin da jihar ke fama da shi wanda ya yi sanadiyyar hallaka mutane da dama tare da lalata tarin dukiyoyi.

“Yayin ziyarar shugaba Tinubu zai gana da dukkan masu ruwa da tsaki da suka hadar masu rike da sarautun gargajiya da shugabanni da malaman addinai da yan siyasa har ma da kungiyoyin matasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here