Mai shari’a Halilu Yusuf na babbar kotun birnin tarayya Abuja, a yau Litinin ya bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele kan kudi naira biliyan 2.
Mai shari’a Halilu Yusuf, ya bayar da belin ne bayan an gurfanar da Emefiele a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume takwas da ake masa shi da karin wasu mutane bisa saba ka’ida da mallakar wani muhalli mai dauke da gidaje 753, da laifin sata da kuma karbar biliyoyin Naira ta asusun ajiyar kudi.
A hukuncin da kotun ta yanke, Mai shari’a Yusuf ya bayyana cewa an bayar da belin Emefiele a kan wasu laifuka uku da ake tsare da shi, kuma babu wata shaida da ke nuna ya tsallake beli.
Daga nan ya ci gaba da sanar da sharadin belinsa da cewa sai ya gabatar da mutum biyu wadanda za su tsaya masa, wanda za su kasance sun mallaki kadarori da ta kai Naira biliyan 2 a cikin Asokoro ko Maitama ko Wuse 2.
Mai shari’a Yusuf ya umurci Emefiele da ya mika takardun tafiyar sa ga kotu sannan ya umarce shi da cewa ya zama wajibi ya kammala cika sharudan belin zuwa ranar Laraba, idan ba haka ba za a ci gaba da tsare shi a gidan yari.
Kotun ta yanke hukuncin ne kan bukatar belin da lauyansa, Matthew Burkaa ya gabatar, wanda lauya mai gabatar da kara Rotimi Oyedepo bai nuna suka ba, amma dai ya bukaci a sauya wasu cikin sharudan belin.













































