Tsohon babban mai bai wa shugaban ƙasa Bola Tinubu shawara na musamman kan harkokin jama’a, Aliyu Audu, ya bayyana cewa ya yi murabus daga gwamnatin shugaban ne domin ya jajirce wajen yaki da sake zaben Tinubu a shekarar 2027.
Audu ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channels ya yi da shi a shirinsa na Sunrise Daily a yau Litinin.
Ya bayyana cewa shawarar da ya yanke ta kasance bisa yaƙini da kuma imani da kasancewar Najeriya za ta samu sauyita, dunkule wuri guda.
Ya caccaki gwamnatin Tinubu kan zargin fifita daukar fansa kan hadin kan kasa, yana mai cewa gwamnatin ta saɓa alkawurran da ta dauka a lokacin yaƙin neman zaɓe.
Audu ya bayyana kawancen siyasa tsakanin Tinubu da Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, a matsayin wanda a da ya zama dole amma yanzu abin tambaya ne.
A gaskiya, akwai dalilai da yawa da suka tabbatar da hakan saboda muna ƙara tunkarar lokacin zablɓe kuma babban abun da ya fi girma a wancan lokacin shi ne tabbatar da cewa mun yi nasara.
Mun san abin da tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya yi a matsayinsa na shugaban kasa yadda ya taka rawar gani wajen daukar yankin Kudu maso Yamma gaba daya, wanda Tinubu ne ke rike da shi a lokacin.
“Wallahi za mu tabbatar da cewa mun sauke shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027. Za mu sake dora shugaban da jama’a suka zaba ba wai wanda aka ƙaƙaba musu ba.













































