Tsohon shugaban karamar hukumar Dala a jihar Kano, Mahmoud Sani Madakin Gini, ya rasu.
Jaridar SolaceBase ta rahoto cewa Madakin Gini, wanda ya kasance shugaban karamar hukumar a zamanin gwamnatin Sanata Ibrahim Shekarau daga 2004-2011, ya rasu ne a wani hatsarin mota a ranar Litinin din da ta gabata a hanyar Kaduna zuwa Abuja, daidai a Kateri, kamar yadda wani abokin sa Umar Ladiyo ya bayyana.
A wata sanarwa da shugaban karamar hukumar Dala Surajo Ibrahim Imam ya fitar, an shirya sallar jana’izar da misalin karfe 5:00 na yammacin yau a gidan su da ke unguwar Yelwa.












































